Header Ads

ad728
 • Breaking News

  HIRAN RABIU BIYORA DA ALJANI UNGURAMI AKAN ZABEN NIGERIA


  YADDA MUKAYI DA ALJANI UNGURAMI A WANNAN DAREN.....

  Malam Biyora ai ban san ka tashi daga wancan unguwar da muka ziyarce ka a kwanakin baya ba, sai bayan danaje gidan sai na tarar babu kowa a ciki, da farko na zata ko kayi tafiya ne kamar yadda na san kanayi a wasu lokutan, amma dana duba dakunan gidan sai na fahimci tabbas tashi kayi, na shiga Halwa ne ta tsawon wata uku, wanda hakan yasa bani da masaniya akan yadda kake tafiyar da al'amuranka kamar a baya, sai da na koma duniyarmu na tambayi Budurwarka ZIRZARA'U sannan take sanar dani inda ka koma har muka tawo tare da ita don ta nunamun gidan naka sannan itama ta samu damar gaisawa dakai kai tsaye, rabon da kuyi magana kai da ita tun a wancan zuwan da mukayi tare da ita, duk da cewa kusan kowanne lokaci tana tare dakai amma bata da ikon yimaka magana ba tare da samun izini daga wajena ba.....

  Da wannan bayanan Dattijon aljani UNGURAMI ya fara, bayan gaisawa da mukayi irin gaisuwar addinin musulunci, mun zauna ni dashi da kyakkyawar aljana Zirzira'u a sabon falon dake tsakiyar gidana, sai yake sanar dani cewa sako na musammam jagora ya sanar dashi wanda ake da bukatar ya riskeni cikin gaggawa musammam dayake ya shafi zaben da zaa gudanar a Nigeria ranar asabar maizuwa, kasan na sanar dakai cewa mu aljanu muna saka idanu sosai akan yadda mutanen Nigeria ke tafiyar da al'amuransu, sannan shi kansa Babban jagoranmu mai martaba DUGUJUN ya kasance yana tare da shugaba Buhari, wanda hakan yasa har ya samar da tutocin jam'iyyar APC a tamu duniyar duk saboda kaunarsa ga shugaba Buhari....

  Kafin in sanar dakai sakon da nake tafe dashi, ina son ka san cewa akwai wasu aljanun da suke tare da jam'iyyar PDP a duniyarmu, hakan ya faru ne sakamakon yakin dake tsakanin masarautarmu da tasu, kuma suna ta kokarin ganin sun temaka wajen kifar da mulkin APC a Nigeria, kai kanka ba tare daka sani ba, budurwarka Zirzara'u kusan kullum sai tayi yaki da aljanu yan PDP dake shirin kawo maka hari don hanaka cigaba da bawa APC gudummawa, hatta tafiyar da kayi bangaren siyasar Atiku Abubakar hakan sai da haifar da babban yaki tsakanin daularmu da daya daular ta yan PDP, domin kuwa Jagora ya huce fushinsa ne akansu, abubuwan da suka faru a sanadiyar wancan abu da kayi suna da yawa, bazanso in sanar dakai gaba daya ba, amma dai nasan bazaka manta yanayin daka samu kanka ba, a wata ranar lahadi lokacin kana zaune a wani hotel dake kumasi Crescent Abuja, basai mun tattauna wannan batun ba, tunda ya Riga ya wuce gaka a tafiyar da muma muke cikinta kuma muka sanka akanta, har ta janyo maka soyayya maiyawa a wajen Mai Martaba DUGUJUN tare da sauran miliyoyin aljanu.....

  Mai Martaba DUGUJUN jagoran miliyoyin aljanu yace in sanar dakai cewa ka gayawa dukkan mutane masoya Shugaba Buhari dasu dage da adduo'i na neman nasara kamar yadda muma mukeyi a yanzu haka, domin akwai babban kalaubale a wannan zaben da zaa gabatar...

  YACE KU KARANTA 

  Surah An-Nasr kafa 3
  Surah al-Mulk kafa 3
  Surah Al-Inshirah kafa 3

  Ranar Juma'a bayan sallar asuba zaa karanta, sai kuma a ranar asabar itama bayan sallar asuba zaa karanta...

  Idan anje filin zabe kafin a dangwala kuri'a sai a karanta Nasrun Minallah Wafathun Qarib sau uku sannan a hada da salatin Annabi SAW sau uku....

  Wannan shine sakon da umarceni in sanar dakai don ka sanar da masoya Shugaba Buhari....

  Zan koma nima don mu cigaba da adduoin neman nasara, sai dai a wannan karon zanso mu dauki hoto tare dakai, amma ka boye fuskata tunda na bayyana ne a siffar bil adam, zan dawo mu karasa shirye shiryen da muke na ziyarar da zaka kai duniyarmu kamar yadda Jagora ya nemi ayi hakan dakai....

  In sha Allah bayan samun nasarar zaben Muhammadu Buhari zamu ziyarci wajen walimar da zaaka shirya, shi kansa Mai Martaba DUGUJUN ya tabbatarmun da cewa zaizo wajen walimar cikin suffar da bazai tsorata masoya Buhari ba....

  Na barka lafiya ka gaishe da dukkan abokanka dake shafukan sadarwar zamani, zan karanta rubutun da zakayi akan wannan ziyarar dana kawo maka, sannan zan turawa da Malamin koyar da Hausa na duniyarmu don ya cigaba da koyawa yaranmu rubutun Hausa, ZIRZARA'U zata cigaba da zama kusa dakai kamar yadda ta saba....

  Sannan mukayi sallama ya bace kamar yadda ya saba a duk sanda ya kawomin ziyara.....

  No comments

  Post Top Ad

  ad728

  Post Bottom Ad

  ad728