Header Ads

ad728
 • Breaking News

  [[Satar Fasaha]] KANNYWOOD KO MASU FASSARA PART I


  KANNYWOOD KO MASU FASSARA PART I

  Daga masoyin Algaita Dubstudio

  ALGAITA MASSUBURBUDA

  Shekarun da suka wuce lokacin da aka fara fassara fim bayan samun karɓuwa da fassarar tayi, shine su kuma yan kannywood saboda hassada suka tashin haiƙan kan cewar sai an daina fassara bisa ga rashin wasu kwararan dalilai, wai satar fasaha ce.

  Sai gashi yanzu kuma basira ta ƙarewa kannywood sun koma satar fasaha. Duk fina-finan kannywood na yanzu rabinsu duk kwaikwayo ne na fina-finan indiya da ƙetare.
  Kwanankin baya Jarumi Adam A Zango shine ke kwaikwayon finan indiya amma sai gashi yanzu duk wani ma'aikaci a kannywood ya koma satar fasaha har shi wanda ake gani a matsayin King of Kannywood wato Ali Nuhu ya koma satar fasaha.

  Akwai fina-finai kamar su:
  1) Umar Sanda
  2) Sagegeduwa
  3) Matan Aure
  4) Zuri'a
  5) Gwaska
  6) Basaja
  Da dai sauransu duk sun kasance fina-finan indiya ne ake kwaikwayo.

  Shi fim din Umar Sanda sun kwaikwayi wani fim ne na Ajay Devgn mai suna Drishyam wanda Algaita suka fassara zuwa ga Dan manya, kuma Ali Nuhu ne a ciki.

  Sai fim din Sagegeduwa sun kwaikwayi fim din Chakwakiyar Aure ne na fassarar Algaita, shima Ali Nuhu ne a ciki.

  Sai fim Zuri'a wanda shima an kwaikwayi fim din jaruma Kareena Kapoor mai suna Family, kuma Kampanin Ali Nuhu ne suka yi fim din.

  Sai Gwaska shima fim din Jarumi Salman Khan mai suna Kick aka kwaikwaya, kampanin Adam A Zango ne suka yi fim din.

  Shima Basaja an kwaikwayi wani fim din Ranveer Singh ne mai suna Ladies vs Ricky Bahl.

  Idan Mukayi duba duk yawancin fina-finan da suke kwaikwaya duk Algaita ta fassara shi, toh kun ga kenan suma suna ƙaruwa da fassarar da ake don na tabbata kaf kannywood babu wanda yake jin indiyanci sai Ali Nuhu shima ba wani sosai ba.

  Sai a cikin Gwaska an kwaikwayi wani bangare daga cikim fina-finan Prabhas Rebel da Billa wato Dan tawaye da Dan Basaja. Akwai wani fim shima mai suna Talaka Bawan Allah na jarumi Ali Nuhu da Ramadan Booth shima an kwaikwayi wani bamgare daga cikin fim din Don no 1 wato Surya Uban daba lamba daya.

  Idan muka yi duba duk wata satar fasaha da suke ikirarin masu fassara sunayi toh yanzu sune suke yi.

  Ku biyo ni a part II domin jin ci gaban wannan sharhi.

  Daga mai kawo labaran Algaita Dub Studio, Naku a koda yaushe Nasiri Muhammad.

  Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

  No comments

  Post Top Ad

  ad728

  Post Bottom Ad

  ad728