Header Ads

ad728
 • Breaking News

  [Rayuwa Y'ar Lissafice] Wurare Biyar (5) da Muke Yin Asarar Kudi ba Tare da Mun Sani Ba


  Wurare Biyar (5) da Muke Yin Asarar Kudi ba Tare da Mun Sani Ba

  Rayuwa a yanzu ‘yar lissafi ce domin randa baka dashi babu mai baka, ya zama dole mu dinga yin nazari a bisa al’amuranmu na yau da kullum, yanzu ana yanayi da wasu na iya yiwa kansu duk abinda sukeso wasu kuma suna zabar mafi muhimmanci suyi saboda yanayinsu, wasu kuwa mai muhimmancin ma basa iya yi.

  Dai dai lokacin da wata ‘yar arewacin Nigeria ta sayi jakar hannu wuri na gugar wuri har sama da Miliyan Biyu ni kuma ina tafene da wasu hanyoyi guda biyar (5) wanda muke rasa kudade ba tare da mun ankara ba.

  1. Cajin da Banki Keyi Mana:- Cajin banki ba karamin barnar kudi mukeyi ba ta nan idan ka lissafa duk kudin da suke cira a yayin da ka turawa wani kudi, ga na SMS da suke turo maka Notifications ga kuma Card Maintenance kuma zaka samu da yawanmu muna da account sama da guda daya, muna dasu a bankuna daban-daban, idan ka lissafa kudin da ake cirar maka nima an cirar min an cirawa Aisha da Mariya shin nawa kake ganin za’a tasa?

  2. Rashin biyan kudi akan lokaci:- idan kaci bashi aka sanya ranar biya baka biya ba, (ba bashin musulunci ba) ko kuma Bill da makamantar siyayya da mukeyi online to indai ka haura akwai abinda ake kara maka akai wanda ake kira Over Time ko Over Due idan ya zama baka biyan irin wadannan akan lokaci to shima zakaga ba kananin kudine mutum yakeyin asara ba, ba tare da ya kula ba.

  3. Hada-hadar yau da kullum:- akwai abubuwan da gabaki daya basu da amfani sai bayan ma ka siya sannan zakaga ba zai maka amfani ba, kuma mafi yawa ana samunsu a kayayyakin rayuwa na yau da kullum, yana da kyau kayi nazari kafin siyan abu, ba komai ne zaka gani ka siya ba, a nan ma muna yin asarar kudi sosai da sosai.

  4. Cinikin Farko:- wannan daman halinmu ne na maza idan mukaje siyan kaya ana fada mana kudin to bama neman ragi kawai sai dai mu bada kudinmu, to shima a nan ba karamin asarar dukiya muke ba, yana da kyau a dinga cizawa sannan abusa yata malam dan hausa.

  5. Subscriptions: - wannan ya hada da na katin waya da na data dama irin wadanda mukeyi na online kamar wanda zakayi na fina-finai ko wakoki da suaran abubuwan da zaka dinga biya ana turo maka, kai harda su Caller Tune da irin na sakonni SMS dinnan da zakayi a dinga turo maka, idan ka hadasu gabaki daya tun daga na wayar zakaga ba karamar dukiyace kake narkar da it aba.

  Allah ya kyauta, ya bamu arzikinmu cikin kwanciyar hankali kuma ya bamu iko da halin rayuwarsa har mu amfanar da wasu.

  Nagoda da ka tsaya ka karanta wannan rubutu nawa.

  Basheer Sharfadi
  Social Media Strategists.
  04-03-2019.
  Email: info@sharfadi.com
  Phone: +2349035830253

  No comments

  Post Top Ad

  ad728

  Post Bottom Ad

  ad728