Header Ads

ad728
 • Breaking News

  YADDA AKE BUDE SHAFIN BLOGGER


  Gabatarwa

  Muna matukar yi muku maraba da zuwa wannan Shafin Namu na maitukunya.com
  Muna kuma  yiwa maziyarta shafin namu fatan alkhairi, Sannan muna taya ku murnar samun wannan dama ta koyon Tsara Shafi (web Desing) a wannan lokacin wanda kowa ya sani cewa akwai dimbim alfanu ga dukkan wanda ya san yanda ake designing na website.

  Ga dukkan wanda ya iya Tsara website, damammakin da ke a gabansa basa kirguwa. Idan ka iya hada website zaka iya hada ma wasu website din kuma su biya ka, zaya iya hada ma kanka website domin ka rika posting akan wani abu da ka sani, a lokaci guda kuma zaka iya samun kudi ta hanyar nuna talla ga mutanen da ke ziyartar shafin naka.

  Baya ga wannan kuma, mutum zai iya hada website domin tallata wani aiki da yake yi ko sana’arsa ko kuma nuna wata fasaha da Allah ya bashi, ko kuma wata akida tasa wacce yake so mutane su san shi akanta.

  Misali:

  Kamar Mai Gidana Basheer Journalist Sharfadi Domin Samun Bayani Akan Sharfadi  Shiga Nan

  A cikin wannna za mu yi amfani da Blogger ne wajen koyar da wannna webdesign. Dalilin da yasa muka zabi blogger shine, idan kana amafani da blogger, babu ranar da zaka ce wai an rufe maka website matukar baka karya dokokinsu ba. Suna ba mutum duk wata dama domin yayi designing din website din shi yanda ya bukata. Kuma sabanin sauran website, blogger suna bada dama mutum ya dora ko wace irin talla yake bukatar dorawa. Wadannan da ma wasu muhimman dalili sune suka sa muka zabi Blogger domin gudanar da wannan darasi.

  1. Opening Blogger ( Yanda ake bude Blogger)

  Da farko dai kafin ka bude blogger account dole ne ka mallaki gmail account. Bayan ka mallaki wannna account sai ka shiga www.blogger.com domin bude website din. Da ka shiga blogger.com, zaka ga akwai inda aka sanya Create your blog. Sai ka danna madannin. Bayan ka danna wannna malatsin, zaya kaika zuwa wani page inda zaka sanya username

  Bayan ka sanya username din sai ka danna Next. Wannan zaya kaika zuwa ga page na gaba inda zaka sanya password. Daga nan zaka wuce zuwa inda za’a tambayeka kalar account din da kake bukatar yin amfani da shi a cikin website din naka. Zaka iya zabar Google+ profile ko kuma Blogger progile .

  Idan ka zabi Google+ profile, za’a kaika wani page inda zaka iya sanya bayananka.

  Sunanka da masu ziyartar shafin zasu gani. Idan kuma Blogger profile ka zaba, shima zaka sanya bayanan, sai ka dannan Continue to Blogger. Wannan zaya kaika ga wani page inda za’a bukaci da ka danna wani malatsi da ke a kasa domin ci gaba.

  Daga nan zaka wuce inda zaka sanya Sunan website dinka wato title da kuma adireshin wannan website.

  Idan ka sanya adireshin dole ne sai google sunyi checking sun ga babu wani mai irin wannan address din, idan kuma akwai mai irin shi zasu gaya maka sai ka sake sanya wani sunan.

  Bayan ka sanya adreshin sai ka zabi Template din da kake bukatar sanya ma website din naka. Template itace kamar copy na website wanda zaka yi amfani da shi wajen kirkirar naka website din.

  Template na dauke da duk wani abun da kake bukata wajen hada website.

  Daga nan da ka danna Create Blog zai kai ka zuwa ga sabon shafinka ko kuma website da kirkira.

  Wadannan sune matakan da kake bukatar ka bi domin ka kirkiri Blogger website da kanka. Abu na farko da zaka fara cin karo da shi shine Dashboard. Yana daga hannun hagu na wannan page da ka bude.

  Shi wannan dashboard shine ke dauke da duk wani abun da kake bukata domin designing da kuma sarrafa shafinka.

  Zamu Dakata Anan Sai a rubutu nagaba zakumu cigaba daga kan Dashboard.

  Daga Muhammad Saminu
  Email: info@maitukunya.com
  Call & Whatsapp 09032313448

  #maitukunya

  No comments

  Post Top Ad

  ad728

  Post Bottom Ad

  ad728